Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na shirin taro a ranar Juma’a mai zuwa don tattauna maganar Korea ta Arewa game da sake gwada harba makaman Roka samfurin Ballistic masu cin gajeren zango.
Kakakin Ban Ki-moon Stephane Dujjaric yace, matsayin da ake ciki na gwaje-gwajen Korea ta Arewa a zirin iyakokin Korea yana da matukar sosa zukata. Saboda haka suna kira ga Pyangyong yin da’a ga dokokin kasa da kasa.
Korea ta Arewa ta hahharba makamanta masu linzami da sunan gwaji, wanda hakan ya sabawa dokar Majalisar Dinkin Duniya, na haramta mata mallakar makaman Nukiliya.
Jami’an gwamantin kasar sun ce Rokar tasu ta ci nisan Kilomita 800 kafin ta tunjima cikin gabashin teku da ke arewaci.