Paraguay ce kasar latin Amurka ta baya bayan nan da ta amince da diyaucin Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kai.
Jiya Jumma’a ce jami’an kasar suka bayyana cewa gwamnatin kasar ta amince da kasar Falasdinu bisa kan iyakokinta kamin a yi yakin da ake kira na “kwana shida”,a lokacinda Isra’ila ta kwace gabashin birnin kudus,da wasu yankunan Falasdinu.
Bada jumawan nan bane,Peru ma ta bada sanarwar ta karbi yankin Falasdinu a matsayin kasamai cin gashin kai,sai dai bata fayyace iyakokin kasar Falasdinun ba.Duk da haka Peru ta amince da wanzuwar kasar isra’ila.
Wasu kasashen Latin Amurka kamar Argentina,Brazil,Bolivis, da Ecuador duk sun bayyana amincewarsu da diyaucin kasar Falasdinu.
Amurka tana sukar guguwar amincewa da kafuwar kasar Falasdinu.Amurka da Isra’ila duk sunce tilas kasar Falasdinu ta kasance wacce aka cimma ta shawarwarin wanzarda zaman lafiya.