Sarki Abdullah na Jordan ya kori gwamnatinsa bayan da aka yi makonni ana zanga zangar bukatar canje canjen harkokin siyasa a kasar. Ya nada wani tsohon janar da umarnin cewa, ya kafa sabuwar gwamnati. Matakin da sarki Abdullah ya dauka martani ne ga zanga zangar da dubban 'yan Jordan suka yi suna bukatar gwamnati ta yi murabus. Gwamnatin da suka dorawa laifin hauhawar farashin mai da kayayyakin abinci da kuma tafiyar hawainiya wajen aiwatar da sauye sauyen harkokin siyasa. Wannan zanga zangar ce ta hadasa zanga zangar da ake yi a Masar da kuma wadda aka yi a Tunisiya 'yan makonnin da suka shige.
Sarki Abdullah na kasar Jordan yakori gwamnatinsa bayan shafe makonni ana zanga zangar neman canji.