Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan sandan kasar Misira sun yi arangama da masu zanga zanga a biranen kasar biyu


Masu zanga zanga kin jinin gwamnati a kasar Misira, suna raira taken kin jinin gwamnati a kwana na uku da fara zanga zanga, a birnin Suez, Jan. 27, 2011
Masu zanga zanga kin jinin gwamnati a kasar Misira, suna raira taken kin jinin gwamnati a kwana na uku da fara zanga zanga, a birnin Suez, Jan. 27, 2011

Yan sandan kasar Misira sun yi arangama da masu zanga zanga a biranen kasar biyu a rana ta uku da fara zanga zangar kin jinin gwamnati.

‘Yan sandan Misira sun yi arangama da masu zanga-zanga a wadansu birane biyu na gabashin kasar, a kwana ta uku da fara gangamin kin jinin gwamnati a fadin kasar. ‘Yan sanda sun yi ta harba barkonon tsohuwa da albarusan roba a kan masu zanga-zanga a Suez, a yau Alhamis. Masu zanga-zanga a birnin sun banka wa wani ginin gwamnati da ofishin ‘yan sanda wuta jiya da wajen almuru. Wadansu kuma sun yi yinkurin kona hedkwatar jam’iyyar National Democratic Party, kafin ‘yan sanda su fatattake su da barkonon tsohuwa. An ji wa akalla mutane hamsin da biyar rauni a wannan tashin hankalin. Haka kuma, daruruwan masu zanga-zanga sun gwabza da ‘yan sanda a birnin Ismaila. A halin da ake ciki kuma wani fitaccen dan gwagwarmayar canji a Misira na shirin komawa ksar. Mohammed El-Baradei, tsohon Shugaban Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya, ya tashi daga Australiya zuwa al-Khahira a yau domin shiga sahun masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Hosni Mubarak da ya shafe shekaru 30 bisa karagar mulki.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG