Dubban masu zanga-zanga sun bazu kan tituna a daidai lokacin da ‘yan sanda ke kokarin hana su tattaruwa a al-Khahira a yau Laraba, kwana guda bayan gungu-gungun masu zanga-zanga da jefe jefen duwatsu su ka mamaye sassan birnin na tsawon awoyi.
‘Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa cincirindon daruruwan masu zanga-zangar da su ka taru tsakiyar birnin. Wasu sun yi ta jifa da duwatsu da kuma konannun tayu a sa’ilinda ‘yan sandan kwantar da tarzoma ke zuba ido.
Hukumomi a Misra sun fadi yau Laraba crewa an damke a kalla masu zanga-zanga 500 a fadin kasar cikin kwanaki biyu din. Kafar yada labarin REUTERS t ace an yi kamen ne cikin kwanaki biyun da su ka gabata.
Tun da farko a yau Laraba Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida t ace ba za a sake bari a yi zanga-zanga ba kuma ta yi gargadin cewa za a gurfanar da masu zanga-zangar.
Duk ko da haramcin, wata kungiyar adawa ta Masar ta yi kiran a sake zanga-zanga a birnin al-Khahira. Kungiyar Matasa ta Tunawa da ran 6 ga Watan Afrilu ta yi amfani da shafinta na Facebook wajen kiran masu zanga-zanga su fito yau Laraba.
Jiya Talata, dubban mutane ne suka shiga zanga-zangar kin gwamnati a birnin al-Khahira da sauran birane, su na kiran a kawo karshen gwamnatin Hosni Mubarak da ta shafe kusan shekaru talatin bisa gadon mulki. Fararen hula uku da wani dan sanda ne aka kashe a zanga-zangar. GwamnatinMisra ta ce ‘yan sanda a kalla 85 sun sami raunuka.
Cikin lumana aka fara zanga-zangar ta jiya Talata, ta yadda da farko ‘yan sanda ke bin abin a hankali. Mutane da yawa sun bayyana cewa rikicin ya barke ne lokacin da masu zanga-zangar su ka nemi kama wata motar tarwatsa zanga-zanga da ruwa.