Ministocin harkokin wajen Tarayyar Turai sun amince da zasu yi wa dukiya da kadarorin hambararren shugaban Tunisia, Zine el-Abdine Ali, da danginsa.
Wan nan mataki ya biyo bayan bukatar da hukumomin Tunisia suka gabatar,majiyoyin difilomasiyya sunce da alamun wan nan mataki zata shafi mukarraban tsohon shugaban kasar. Ana zargin Mr. ben Ali da arzurta kansa dad a dukiyar kasar yayinda yake mulki.
Babu tabbas kan ainihin inda dukiyarsa take.
Idan za’a iya tunawa ranar 19 ga watan Janairu ne Swizteland ta bada snarwar ta yi wa dukiya da kadarorin tsohon shugaban Tunisiyan daurin talala.