Ana sa ran shugaba Trump zai tabo batutuwan da zai fi maida hankali akan su a kasafin kudin shekara mai zuwa, ciki har da batun karawa fannin tsaro karin kudade da kuma zaftare kudaden tallafin da Amurka ta ke baiwa kasashen waje da ma wasu shirye-shirye na cikin gida.
Yayin wani taro da suka yi da gwamnonin jihohin kasar jiya a Fadar White House, shugaba Trump ya ba da somin-tabin abinda jawabin na sa na yau zai kunsa.
“Wannan kasasfi kudi zai zamano wani mataki na cika alkawarin da na yin a maida hankali wajen samar da tsaro a Amurka, da tsare ‘yan ta’adda shiga kasar nan da fitar da bata-gari da masu aikata manyan laifuka daga kasarmu baki dayansu.” In ji Trump.
Baya ga kara kudade ga fannin tsaro da rage kudaden da ake kashewa a cikin gida, ‘yan majalisun dokokin Amurka suna sa ran shugaba Trump zai tabo batun haraji da bangaren kiwon lafiya,a cewar mai fashin baki John Fortier.
“Shugaba Trump da ‘yan jam’iyarsa ta Republian, sun amince su kawar da tsarin kiwon lafiya nan na Obamacare da kuma rage kudaden haraji tare da samar da tsaro a kan iyakokin kasar, saboda haka ire-ire wadannan batutuwan zai nemi hadin kan ‘yan jam’iyarsa akai.” Fortier.
Sai dai kamar yadda rahotanni suke nunawa, ‘yan jam’iyar Democrat, a shirye suke su kalubalanci kusan daukacin manufofin gwamnatin ta Trump kamar yadda sabon shugaban jam'iyar Tom Perez ya sha alwashi.
Masu lura da al'maura da dama, suna ganin wannan wata dama ce da Trump ya samu da zai iya kyautata dagantakarsa da 'yan majalisun.
Facebook Forum