Babban jami’in yayi gargadin ne a wajen bude taron hukumar kare hakkin bi’l Adam karo na talatin da uku a Geneva.
Yace duniya zata yi hasara idan aka saurari kamfe da shugabannin siyasa suke yi kan take hakin bi’l Adam ko kuma barazana da suke yi ta janyewa daga wadansu yarjejeniyoyi da aka kulla da kuma cibiyoyi dake goyon bayan irin wadannan ‘yancin.
Antonio Guterres wanda yake halarton taron karon farko a matsayinsa na babban magatarkar MDD ya bayyana damuwa a kan abinda ya bayyana a matsayin halin ko in kula da ake nunawa abinda ya shafi kare hakkin bi’l adama a duk fadin duniya.
Yayi gargadi da cewa, keta hakin bi’l Adama alama ce ta tashin hankali. Yace hakin kowa ne a dauki matakin ganin ba a sami tashin hankali ba. Yace tilas ne a saurari koke keken al’umma a kuma dauki matakan gaggawa na shawo kansu yadda ya kamata.
Facebook Forum