A jihar Nasarawa kuwa, ma’aikata sun ce basu da dalilin farin ciki saboda rashin biyansu cikakken albashi na wasu watanni.
Shugaban kungiyar ma’aikatan jihar Nasarawa Abdullahi Adeka, ya fadawa shaidawa sashen Hausa na Muryar Amurka cewa da yawa daga cikin ma’aikatun jihar sun kwashe watanni biyar ba tare da sun biya ma’aikata albashinsu ba.
Wata ma’aikaciyar ‘karamar hukuma a jihar Nasarawa da ta bukaci a sakaye sunanta, ta ce ma’aikata a jihar na cikin ‘ka ‘ka na kayi.
Sai dai kwamishinan yada labarai da raya al’adun gargajiya a jihar Abdulhamid Yakubu Kwara, ya ce ya san cewa ba a biya albashin watan biyu ba, kasancewar akwai yarjejeniya tsakanin gwamntin jiha da kungiyar kwadago, na cewa idan wata ya ‘kare kudaden da ke ‘kasa ba zasu isa a biya albashi ba, to za a jira har sai watan gaba abin da ya samu sai a hada baki daya a biya albashin.
A cewar gwamnan jihar Nasarawa Umaru Tanko Almakura, ya bayyana matsalolin da suka jefa ma’aikatan jihar cikin halin ‘ka ‘ka na kayi, inda yace yawan daukar ma’aikatan da suka wuce ‘kima a kowacce ‘karamar hukuma shine ya haddasa rashin isasshen kudin da za biya ma’aikata albashi kan lokaci.
Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.
Facebook Forum