Biyo bayan rahoton da hukumar ‘yan Sandan Najeriya ta fitara makon daya gabata cewa ta gano wasu takardu a gidan tsohon gwamnan jihar Gombe Sanata Muhammad Danjuma Goje, a lokacin da suka je wani bincike gidansa dake Abuja, wanda a ciki akwai me nuni da cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon Ministan Ilimi, Malam Ibrahim Shekarau, na da hannu a kisar gillar da aka yiwa Sheik Ibrahim Ja’afar, yafara haddasa muhawara da kuma tsokaci a tsakanin mutane.
Jihar Gombe kasancewa daga nan ne Sanata Danjuma Goje, ya fito a yawancin wuraren zaman jama’a, batun takardun da aka samo a gidan Danjuma Goje, shi suke juyayi akai, kwamrade garba Tela, cewa yayi abinda aka yi a Kano me zai kawo shi Gombe, kai dai abinda aka je nema ba a samu ba sai aka fake da wani abun.
Ya kara da cewa mai hankali ya san cewa wannan wani al’amari ne wanda bai ma shafi cewa yana da hannu a kisar Malam ja’afar, ba ko alama shi ba jahili ne ba da zai rike takardu irin wadan da ake batu akai da jin wanna ya kamata mai hankali ya yi tambaya.
Wani Lauya mai zaman kansa Abdullahi Muhammad Inuwa, yace ‘yan Sanda sun nuna gazawa domin a doka kafin ace mutun yayi laifi dole ne sai akwai sheda a kansa amma cewa wai an samu takarda a wajensa shin an bashi ajiya ne ko kuma shi mene ne nasa a ciki domin haka ‘yan Sanda basu yi aikin da yakamata ba.
Ya kamata ace hukumar ‘yan Sanda sai tayi bincike kuma ta tabbatar cewa ta samu wani sheda mai karfi kafin har ta fito ta gayawa duniya.
Wani Lauya mai suna Yunusa Muhammad Morocco, yace hukumar ‘yan Sanda tana aikinta ne saboda haka jama’a, su daina jita jita, dalili yake ‘yan Sanda gidan saboda haka sai sun kammala binciken su domin hakkin ne da tsarin mulki ya dora masu.
Facebook Forum