Sakamakon rikicin kungiyar Boko Haram fiye da ma’aikata Dubu ‘daya ne suka rasa rayukansu a jihar Borno, a cewar shugaban kungiyar Kwadago na jihar, Kwamarad Titus Ali Abana, shugaban ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da Muryar Amurka.
Kwamarad Titus, ya ce ma’aikata da yawa sun rasa rayukansu musamman ma dai malamai wanda adadinsu ya kai kimanin 500 da m’aaikatan jinya da kuma sauran ma’aikata da ke zama ‘ya ‘yan kungiyar kwadago, inda ya ce zasu gudanar da bikin bana don jimami da kuma tunawa da su.
A Najeriya ma’aikata daga bangarori daban-daban sun shiga halin ‘ka ‘ka na kayi cikin shekaru biyun da suka gaba sakamakon rashin kwanciyar hankalin da ya addabi shiyyar Arewa maso gabashin kasar.
Jihar Borno na ‘daya daga cikin jihohin Najeriya da ma’aikata ke bin gwmnati bashin albashi ko alawus. Suma ma’aikatan da suka yi ritaya har yanzu sun bin gwamnatin jihar bashi kudaden fansho a cewar kwamrad Titus Ali Abana.
Domin karin bayani saurari tattaunawar Kwamrad Titus Ali Abana da Haruna Dauda.
Facebook Forum