Amurka ta bada sanarwa Karin tallafin dala miliyan talatin domin tallafawa al’umar yankin arewa maso gabashin Najeriya inda aika aikar tsagerun ‘yan Boko Haram ya haddasa matsaloloin jinkai barkatai.
Wannan Karin taimako zai marawa shirin majalisar dinkin duniya na samarda tallafin nau’oin abinci daban daban da kuma agajin kudaden siyan abincin a yankunan da yanzu ake hada hadar kasuwanci.
Za kuma ayi amfani da wani bangare na kudaden wajen tallafawa komawa aikin gona ga al’umomin da zaman lafiya dore a yankunansu a halin yanzu.
Tun daga watan Oktoba na shekarar 2015, Amurka ce ke kan gaba wajen samarda tallafin jinkai a kasashen yankin tafkin Chadi inda ta bada taimakon zunzurutun kudi har dala miliyan dari hudu da hamshin da biyu ($452) ga jama’ar da wannan ja’ibar wannan tarzomar ta Boko Haram, ta rutsa dasu.
Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ta fitar ta nuna cewa amurkan zata ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin Najeriya da sauran kungiyoyin jinkai domin samarda taimako a kaucewa ja’ibar yunwa sannan a marawa al’umomin dake cikin mawuyacin hali.
A bayan dai Majalisar dinkin duniya, ta yi gargadin cewa muddin bai ayi wani abu cikin gaggawa ba toh yunwa ka iya tagayyara miliyoyin mutane kuma tana iya kasancewar miliyoyin kananan yara su rasa rayuwarsu.
Facebook Forum