A karon farko hadakar kungiyoyin maharban Najeriya shiyar arewa maso gabashin kasar sun dunkule wuri guda domin taimakawa wajen yaki da masu tada kayar baya na Boko Haram,barayin shanu da kuma masu garkuwa da mutane domin samun kudin fansa.
Wannan mataki ya biyo bayan sabanin da aka ta samu ne a rassan kungiyar na wasu jihohi ,kuma wannan na zuwa ne yayin da ake haramar kawo sauyi da canje-canje a kungiyar maharban Najeriya.
Ba tun yau bane dai aka san maharba da taka muhimmiyar rawa wajen yaki da bata gari a tsakanin al’umma,kamar yadda suka taka a yaki da 'yan bindiga masu tada kayar baya na Boko Haram a 'yan shekarun nan.
Sai dai kuma yayin da ake yaba musu wata matsalar dake neman maida hannun agogo baya itace ta rabuwan kawuna a wasu jihohi na arewa maso gabashin kasar,batun da yanzu wasu shuwagabanin kungiyar a Najeriya gudanar da wani taro na kawo fahimtar juna domin hadewa karkashin inuwa guda,wato kungiyar maharban arewa maso gabas da ta kunshi jihohi shida,wato jihohin Adamawa,Bauchi,Borno,Gombe,Taraba da kuma jihar Yobe.
A karshen wani taron da suka gudanar shugabanin kungiyar bisa jagoranci,Alh.Muhammad Usman Tola sun saba layar cewa zasu cigaba da bada gudumar da suke badawa a yaki da yan Boko Haram,da masu garkuwa da mutane kana da masu satar shanu,batun da ke neman gagaran kundila inda shugaban kungiyar maharban na jihohin arewa maso gabas,Muhammad Usman Tola ya bukace su da a yafewa juna.
Shiko Alh. Nasiru Adamu Doya –shine shugaban kungiyar na jihar Bauchi ya tabo irin gudumawar da suke baiwa jami’an tsaro ne da cewa suna aiki tare da jami’an tsaro kuma zasu cigaba da tallafawa.
A wasu jihohi dai rabuwan kanuwa a tsakanin maharban ya kan jawo ci-baya, inda Sarkin Bindiga Micheal Pupule daga jihar Taraba yace ,ya bada misali da abun dake faruwa a jiharsa.
To sai dai kuma Muhammad Ibrahim dake zama wakilin Sarkin Bakan Gombe kuma sakataren riko na hadakar kungiyar a shiyar arewa maso gabas ,yace da wannan taron an dinke barakar dake akwai a tsakanin rassan kungiyar na jihohi.
Baya dai ga batun zama tsintsiya madaurinki guda, maharban sun gudanar da abun da aka saba,na nuna kwari da kwankwamai.
Facebook Forum