Daruruwan magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar Bayelsa sun gudanar da zanga-zangar lumana a yau Lahadi a birnin Yenagoa domin nuna adawa da sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar a Nembe-Bassambiri, dake karamar hukumar Nembe.
Sun yi zargin cewa ba a yi zabe a Nembe-Bassambiri ba, don haka sakamakon zaben da aka fitar a wurin na boge ne.
Da misalin karfe 9:30 na safe ne masu zanga zangar suka tattaru a filin taro na Isaac Boro Peace Park, kana suka zaga wasu titunan zuwa ofishin hukumar INEC na jihar Bayelsa dake kan hanyar kasuwar Swali Market.
Sai dai yayin da masu zanga-zangar suka tunkari titin Swali daga titin Lambert Eradiri suka wuce shataletalen da ke hade da titin Mgbi, jami’an tsaro da dama dauke da makamai sun kafa shingen binciken a kan titin Swali suka hana isa kusa da kofar shiga ofishin INEC.
Jami'an tsaron sun tare hanyar ne tare da wasu rundunar tsaro masu makamai da wasu motocin sintiri a yayin da kuma suka dauki matakai masu mahimmanci a kewayen yankin.
Da yake magana a wata hira da manema labarai kwamishinan ilimi na jihar Gentle Emelah ya ce sun gudanar da zanga-zangar ne saboda an hana ‘yan jam’iyyar PDP masu cancantar kada kuri’a a Nembe-Bassambiri kuma hakan ba za a lamunta da shi ba.
Ya yi kira ga INEC da Kwamishinan Zabe na Jihar, Obo Effanga, da su yi watsi da sakamakon Nembe-Bassambiri, yana mai jaddada cewa ba a yi zabe ba a wannan wurin.
Wakilin Sashen Hausa a Bayelsa, Lamido Abubakar Sokoto shima ya hada rahoto a cikin sauti a kan hanlin da ake ciki yayin da ake dakon sakamakon zaben.
Rahoto cikin sauti:
Dandalin Mu Tattauna