India da Uzbekistan suna cikin kasashen da suka fi yawan mutanen da ake bautarwa. Al’ummar Uzbekistan suna fuskantar yanayin bauta inda hukuma ke tilasa su cirar auduga.
Koriya ta arewa ita ma tana cikin jerin kasashen dake da bayi tsakanin al’umma inda ake bautar da fursunoni, da tilastawa wadansu karuwanci da kuma auren dole.
Lamarin yafi sauki a kasashen dake da arziki, kasashe goma sha biyu da matsalar bata yi Kamari ba sun hada da kasashen yammacin Turai, Amurka, Canada da Australia, da New Zealand. Sai dai binciken ya kuma nuna cewa, Qatar, Singapore, Kuwait, Brunei, Hong Kong, Saudiya, Baharain, Oman, Japan da kuma Koriya ta Kudu suna cikin jerin kasashen da gwamnatocinsu basu dauki matakin a zo a gani ba, dangane da bauta irin ta zamani, duk da arziki da kuma ci gabansu.
Binciken yayi la’akari da batutuwa kamar karewa da kuma mutunta bil’adama, da kula da lafiyar al’umma da tsaro da samun muhimman ababan more rayuwa kamar abinci da ruwan sha da kula da lafiya, da yanayin kaura, da kuma rikici.
An gudanar da wannan binciken a kasashe dari da sittin da bakwai. Sai dai ba a bada sakamakon binciken Afghanistan da Iraq da Libya da Somalia da Syria da kuma Yemen ba, sabili da rikici da ake yi a kasashen.