Jiya ranar hutu ce a duk fadin kasar Amurka inda shugaban kasar ya kira amurkawa da su tashi su taimakawa iyalan sojojin da suka kwanta dama saboda sun sadakar da rayukansu ne ma kasar domin ta rayu.
Shugaba Obama yace kasa kan bayyana kanta ne ba da irin mutanen da take dasu ba kawai har ma da wadanda take tunawa dasu.
A makabartar Arlington ta ksa inda ake binne shugabannin Amurka da sojojin da suka kwanta dama, Shugaba Obama ya ajiye fure kan kabarin sojan da ba'a sani ba. Yace "muna yin hakan ne ba wai mu daga tutarmu ba kawai amma domin mu tallafawa makwaftanmu. Mu taimakawa makwaftanmu ta yadda zamu nuna 'yanci da kamanta juna tare nuna cewa daya muke domin a kan wadannan ne sojojinmu suka sadakar da rayukansu.
A wannan bikin tunawa da mazan jiya wanda ya kasance masa na karshe kafin ya cika wa'adin mulkinsa watan Janairu mai zuwa, Shugaba Obama ya lura kasa da kashi daya cikin dari na amurkawa ne suke aikin soja. Wannan na nufin cewa akwai miliyoyin amurkawa da basu san kowa a cikin sojojin yanzu ba.
Yayinda yake makabartar, shugaba Obama ya lura da yadda wurin yayi tsit saboda babu motsin mutum, babu motsi a anguwar matattu. Ya lura da sashena 60 a makabartar inda cikin 'yan shekarun nan aka binne sojojin da suka rasa rayukansu a Gabas ta Tsakiya.
Yace " mu da muke da rai, muna da murya, wajibi ne mu cike gurbin da suka bari da kauna da goyon baya da kuma godiyarmu da kalamu da kuma aiwatar da abubuwan da zasu taimaka, inji Shugaba Obama.
Hanyar da zamu nuna muna tunawa da wadannan da suka kwanta dama ita ce ta taimakawa iyayensu da matansu ko mazansu da kuma 'ya'yan da suka bari baya, inji Obama.