Muhammad Alloush babban shugaban 'yan tawaye a wurin taron neman sulhu a rikicin Syria da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya, ya sanar jiya Lahadi cewa zai janye daga tattaunawar.
Alloush yace ya yanke shawarar janyewa ne saboda cigaba da yaki da dakarun gwamnatin kasar Syria suke yi, tare da taimakon kasar Rasha, soboda kare shugaban kasar Bashar al-Assad. Nufin Rasha ne ta tabbatar shugaban ya cigaba da kasancewa kan mulkin kasar ko tahalin yaya.
Alloush babban jigo kuma mai fada a ji na babbar kungiyar tawaye mai suna Jaish al-Islam ya bada misali da taurin kan gwamnatin al-Assad da yadda take cigaba da kai hare hare kan al'ummar kasar Syria tare da cin zarafinsu.
Tattaunawar makonni biyu a birnin Geneva inda jami'an Majalisar Dinkin Duniya suka gana da wakilan gwamnatin al-Assad daban da kuma wakilan 'yan tawaye daban bai cimma wata yarjejeniya ba, a akasarin kaskiya ma yaki tsakanin bangarorin biyu sai kara tsamari ya keyi.
Shirin tattaunawa karo na uku da aka so a yi a karshen watan Mayu bai tabbata ba. Makon jiya wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman Staffan de Mistura yace ba za'a sa wata sabuwar ranar da za'a sake zama ba sai bangarorin biyu sun amince da tsagaita wuta tare da barin kayan jinkai su isa dubun dubatan mutane , yawancinsu farar hula, da suka tagayyara.