Shi Lieberman dai dan jam'iyyar Yisrael Beitneu ne,jam'iyyar da tayi kamarin suna a kasancewa mai matsanancin ra'ayi.
Jam'iyyar ce ta hada kwance da ta Firayim Minista Netanyahu har suka kai ga kafa gwamnatin hadin gwuiwa. Mr. Lieberman ya taba rike makamai daban daban har da na ministan harkokin waje.
Lieberman shi ya kira a jefa bamabamai kan sansanin Falesdinawa kuma ya yi kokarin hana jam'iyyun Larabawa daga shiga zabukan kasar. To saidai Lieberman wanda aka sanshi da daukan tsauraran matakai akan Larabawa, yace ya yadda da shirin samun kasashe biyu masu cin gashin kansu wato, Israila da Falesdinu a yankin Gabas ta Tsakiya.
Ya fada jiya Litinin cewa ya yadda da Firayim Minista Benjamin Netanyahu wanda ya dukufa da samun zaman lafiya da makwatansu da suka hada da Falesdinawa.
Netanyahu yace a shirye yake ya sake tattaunawa akan shirin Larabawa wanda zai yi la'akari da wasu cajnje-canje da suka faru a yankin tun shekarar 2002.
Duk da kalamun sassauci da suka fito daga gwamnatin da ake ganin ta masu ra'ayin rikau ne, wani mai magana da yawun Falesdinawa yace kawo Lieberman mai matsanancin ra'ayi cikin gwamnatin Israila tamkar gauraya matsanancin ra'ayi ne da hauka.