Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 39 Sun Mutu Sakamakon Gobara A Wata Cibiyar 'Yan Cirani Dake Kan Iyakar Mexico Da Amurka


Gobara A Cibiyar ‘Yan Cirani A Mexico
Gobara A Cibiyar ‘Yan Cirani A Mexico

Fiye da bakin haure talatin da tara ne suka mutu sanadiyyar gobara a wata cibiyar ajiye bakin haure da ke arewacin Mexico a kusa da kan iyakar Amurka, in ji wani jami'i ranar Talata.

WASHINGTON, D.C. -Hotuna daga wurin da gobarar ta tashi sun nuna jerin gawarwaki dake kwance a wajen cibiyar dake garin Ciudad Juarez, daga El Paso a jihar Texas. Sannan an ga motocin daukar marasa lafiya, da ma'aikatan kashe gobara, da ma manyan motocin daukar gawarwaki a wurin.

Gobara A Cibiyar ‘Yan Cirani A Mexico
Gobara A Cibiyar ‘Yan Cirani A Mexico

Mutane 39 ne suka mutu yayin da 29 suka jikkata sakamakon gobarar da ta tashi da yammacin ranar Litinin, kamar yadda wani jami’in hukumar kula da shige da fice ta kasar ya bayyana, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba a ba su izinin yin magana a kan batun ba.

Birnin Ciudad Juarez wani babban mashigi ne da bakin haure ke ratsawa su shiga Amurka. Cibiyoyin tsugunnar da jama'a na birnin na cike da baki da ke jiran samun damar tsallakawa ko kuma wadanda suka nemi mafaka a Amurka dake jiran bin tsarin.

Gobara A Cibiyar ‘Yan Cirani A Mexico
Gobara A Cibiyar ‘Yan Cirani A Mexico

Ofishin babban lauyan Mexico ya kaddamar da bincike kuma ya tura masu bincike a wurin da gobarar ta auku, kuma an kira Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta kasa don taimakawa bakin hauren, a cewar rahotannin kafafen yada labarai.

-AP

XS
SM
MD
LG