Hukumomi a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya sun gudanar da jana’izar mutum 50 da suka hada da ma’aikata da ‘yan kasuwa, wadanda gobara ta rutsa da su a wata haramatacciyar matatar mai, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.
A ranar Juma’a wata gobara ta tashi a matatar man wacce ke yankin Obaezi a karamar hukumar Ohaji-Egbema.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA ta ce akalla mutum 110 ne suka mutu, ko da yake wasu majiyoyi na ikirarin adadin zai fi haka.
Shugaban matasa a yankin Bright Onyenwoke ya ce, da yawa daga cikin iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, sun dauki gawarwakin ‘yan uwansu sun yi musu jana’iza.
Hakan ya sa hukumomin suka yi jana’izar ragowar gawarwaki 50 a ranar Talata.
Najeriya ita ce kasar da ta fi samar da man fetur a duk nahiyar Afirka, inda har akan samu haramtattun matatun mai da ake ginawa a dazuka, lamarin da ke haifar da asarar rayuka da mummunan ta’adi.
Bayanai sun yi nuni da cewa, jami’an tsaron kasar na farautar wasu mutane biyu da ake zargi na da hannu a ibtila’in.
Ko da yake, jami’an yankin na zargin jami’an tsaro da hada kaia da masu aikin haramtattun matatun man.