Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Girka Sun Kwashe 'Yan Cirani a Tsibirin Lesbos


Wasu daga caking 'yan gudun hijirar da ke zaune a sansanin Moria da ya yi gobara
Wasu daga caking 'yan gudun hijirar da ke zaune a sansanin Moria da ya yi gobara

Bayan da suka kwashe wasu kwanaki cikin mawuyacin hali a kasar Girka an kwashe 'yan cirani da 'yan gudun hijira zuwa wani matsuguni bayan da sansanin da suke zaune ya yi gobara.

Hukumomi a tsibirin Lesbos da ke kasar Girka, sun kwashe wasu ‘yan cirani da ‘yan gudun hijra 300 da ba su da matsuguni, inda aka kai su wani wuri na wucin gadi, bayan da gobara ta lakume sansanin da ake kira Moria mai cunkoson jama’a.

Lamarin ya bar masu neman mafaka dubu 12 ba tare da matsuguni ba - a wannan yanayi mafi girma da kasar ta Girka ba ta taba gani ba cikin shekara biyar da suka gabata.

A ranar Lahadin nan an ga ‘yan gudun hijra sun yi jerin gwano a kofar wurin da ake kira Kara Tepe - inda nan hukumomi suka kebe masu a matsayin wurin zaman na wucin gadi, bayan da suka kwashe kwana hudu cikin mummunan yanayi.

An ga da yawa daga cikin ‘yan ciranin dauke da jarirai, da ‘yan jakunkuna leda da suka zuba kayayyakinsu da suka iya kubutarwa kafin gobarar ta ci karfin sansanin nasu da suka baro.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG