N’KONNI, NIGER -Tuni dai hukumomin Nijar suka aika tawaga a wannan garin, domin jajanta wa wadanda abin ya shafa da al'ummar wannan garin da suka ce, ba su taba ganin wani iftila'i da ya shafi iyali guda ba kamar wannan.
Mutanen, ‘yan gida daya ne su biyar, da matar mai gida da yaranta hudu, da mai aikin gidan da wani makwabci da ya kawo dauki suka rasa rayukansu a gobarar.
Abin dai ya faru ne a alokacin da mai gidan ke Yamai, babban birnin kasar, dake makwabtaka da jihar Dosso wurin wani aiki.
A daidai lokacin da abin ya faru dai, yan kwana-kwana sun kai dauki tare da makwabta da sauran jami'an tsaro na garin na Gaya.
Kaftin Guero Mahamadu, wanda shi ne shugaban rundunar 'yan kwana-kwana na garin na Gaya, ya ce abin yayi muni sosai, domin mutane bakwai sun rasa rayukansu, matar gidan da mai aikinsu da 'ya’yanta da wani da yazo kawo dauki.
Ya ce lokacin da muka iso, har falon ya dauki wuta, kuma wuraren shiga duk like suke, domin mutanen na cikin dakuna uku, yayin da wadanda ke ciki, hayaki ya rigaya ya raunana su.
Sanadin gobarar shi ne, baskin wutar lantarki a cikin falon gidan, kuma tuni hukumomin kasar suka tura tawaga a karkashin jagorancin gwamnan Jihar Dosso, Malam Albachir Aboubacar, domin zuwa garin na Gaya da jajantawa iyalai da hukumomin garin game da wannan lamarin da suka ce basu taba ganin irin sa ba.
Gwamnan na cewa, “na kadu sosai game da wannan iftila'in, domin dukkan iyalai guda ne abin da ya rutsa da su a lokacin da mai gidan ke cikin balaguro. Yanzu haka dai, ana cikin bincike game da musabbabin wannan gobarar, haka ma, ina isar da sakon ta'aziyya ga wannan iyalin da suma mahukunta na wannan kasar, tare da basu hakuri da su, da ‘yan uwa da aminan arziki da fatan Allah ya jikan wadanda suka rasu.”
Wannan mumunan lamarin ya lausar da jikin mutanen Gaya dake ci gaba da isa gidan mamatan domin isar da sakon ta'aziyyarsu.
Saurari cikakken rahoton daga Haruna Mamane Bako: