Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyu Sun Amince Carles Puigdemont Ya Yi Takarar Shugaban Kasa A Catalonia


Taron 'yan majalisa na farko a Catalonia bayan zabe
Taron 'yan majalisa na farko a Catalonia bayan zabe

Gwamnatin yankin Catalonia ta yi zama na farko a bayan zabe kuma har ta amince da goyon bayan wanda zaiyi takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

A karon farko tun bayan da gwamnatin kasar Spain ta rusa gwamnatin yankin Catalonia, majalisar dokokin zata zauna bayan zaben da ya biyo bayan matakin sakamakon yunkurin ballewar da yankin ya ayyana ta wajen kaddamar da kuri’ar raba gardama.

Jam’iyu masu ra’ayin ballewa suna da ‘yar rinjaye a sabuwar majalisar, amma wajibi ne wakilan majalisar su kafa gwamnati sannan su zabi shugabannin su.

Gabannin zaman na yau, jam’iyu biyu masu ra’ayin ballewa sun cimma jarjejeniyar zasu goyi bayan tsohon shugaban yankin Carles Puigdemont a zaman dan takara a zaben shugabannin da zasu jagoranci yankin.

Prime Ministan Spain Mariano Rajoy, yace ba za’a tsaida Puigdemont zaman dan takara ba saboda yana gudun hijira, kuma idan aka zabe shi to gwamnati zata ci gaba da aiki da dokar dakatar da diyaucin yankin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG