Shugaban sojoji da suka yi juyin mulki a Mali Amadou Sanogo, yace rundunar mayakan kasar tana ci gaba da mutunta dukkan yarjejeniya da kasar ta kulla da kungiyar raya tattalin arzikin kasashe dake yammacin Afirka watau ECOWAS, da sauran kawayenta ta fuskar tattalin arziki.
Sanogo ya gayawa sashen faransa na Muriyar Amurka a hira da aka yi dashi ta woyar tarho cewa, Mali memba ce ta kungiyar ECOWAS kuma tana bukatar taimakon kasa da kasa domin kare diyaucin kasar, yayinda ‘yan tawayen abzinawa suke ci gaba da dannawa cikin kasar. Ya bayyana takaicin ganin ba’a sami ganawa tsakanin wakilan kungiyar ta ECOWAS da na gwamnatinsa ba.
Shugaban yace Mali ita kadai ba zata kai labari ba, tana bukatar taimakon kasashe makwabta. Ya kara da cewa suna bukatar gudumawar kungiyoyin kasa da kasa da kuma kwayen Mali a cikin wan nan lokaci na mawuyacin hali da kasar ta shiga.