Ministan kwadago da samar da ayukan yi, Sanata Chris Ngige ne ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabijan na Channels a ranar Lahadi bayan wata ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke birnin Abuja.
A cewar Ngige, ya zanta da shugaba Buhari kan yanayin da ake ciki kuma sun cimma matsayar cewa ya kamata likitocin su dawo bakin aiki, ita kuwa gwamnati za ta janye karar da ta shigar a gaban kotu.
Gwamnati dai ta ce ba zata lamuncewa duk wani abu da zai sabawa kundin tsarin mulkin kasar ba, amma a shirye ta ke ta janye karar idan likitocin sun janye yajin aikin da su ke kai a halin yanzu.
Ngige ya kuma kara da cewa wasu ma’aikata sun yi asarar albashinsu a yayin yajin aikin da suka gudanar a baya karkashin dokar “babu aiki, babu biyan albashi” kuma gwamnati zata hukunta likitocin da ke yajin aiki idan suka ki komawa bakin aiki.
"Ma’aikatan da suka yi asarar albashinsu a lokacin yajin aikin na shekarar 2018 sun hada da hadakar kungiyar ma’aikatan kiwon lafiya wato JOHESU sakamakon kwashe watanni hudu a yajin aiki kuma suka yi asarar kusan albashin watanni biyu ko uku lokacin da aka yi amfani da dokar ‘ba bu aiki, babu albashi” in ji Ngige.
Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnati na duba lamarin jerin likitoci dubu 8 da za su ci gajiyar asusun horar da ma’aikatan kiwon lafiya a halin yanzu.