Yajin aikin kungiyar likitocin ya zo ne kwanaki 113 bayan da ta janye yajin aikin da ta shiga a can baya, a cewar shugaban kungiyar Okhuaihesuyi Uyilawa.
Likitocin sun shiga yajin aikin ne kan korafe-korafe da suka hada jinkirin biyan albashi da alawus-alawus, karancin ma’aikata a asibitoci da kuma rashin ingantaccen yanayin aiki yayin da ake kara samun yaduwar annobar korona a kasar.
Shugaban kungiyar yace wannan karon ba gudu babu ja da baya har sai gwamnati ta biya wa kungiyar ta NARD bukatunta.
A wata sanarwa da hukumar lafiya ta kasar ta fitar kan yajin akin, Ministan Lafiya Dr. Osagie Ehenire yayi kira ga kungiyar likitocin dasu sassauta don a sami warware lamarin cikin ruwan sanyi, kada a samu koma baya a aikin kiwon lafiya.
Yajin aikin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke kara samun masu kamuwa da cutar korona da kuma barazanar barkewar cutar cholera a wasu yankuna.