Ngige ya yi wannan kiran ne a yayin da ya ke sharhi a cikin shirin siyasa na gidan talabijan na Channels a ranar Lahadi, a yayin da yajin aikin likitoci ya shiga rana ta 59.
Ya kin mutunta umarnin kotu ka iya zama raini ga bangaren shari'a a kasar.
Saboda haka ya yi kira ga kungiyar da ta sake duba matsayarta, ita da mambobinta su koma bakin aiki yau Litinin ko kuma gobe Talata, kana daga nan su koma kan teburin tattauna muhimman abubuwa da dama da ke tsakaninsu.
Ministan ya kuma yi sharhi kan karar da gwamnatin tarayyar ta shigar a gaban kotu kan likitocin da ke yajin aiki, ya na mai cewa ma’aikatar lafiya da ofishin ministan shari'a za su dauki matakin da ya dace kan lamarin.
Ngige ya kara da cewa ya shawarci abokin aikinsa a ma'aikatar Lafiya, Dakta Osagie Ehanire don yin shawara kan zaman tattaunawar, kuma ya ce a kullum yana ba da shawarar a bi hanyar sasantawa don mafita.
Kalaman na Ngige na zuwa ne kwanaki biyu bayan kwarya-kwaryan hukuncin kotun masana’antu ta kasar, inda ta umarci likitocin da su dakatar da yajin aikin su sannan su koma bakin aiki, har zuwa lokacin da za a yanke hukunci.
A radar juma’a da ta gabata ne mai shari’a Bashar Alkali ya yanke wannan hukuncin bayan bukatar da gwamnatin tarayya ta mika a gaban kotu kan lamarin, saidai likitocin da ke yajin aiki sun yi fatali da hukuncin kotun, inda suka sha alwashin daukaka kara.