ABUJA, NIGERIA —
A shirin Tubali na wannan makon mun tattauna kan yadda Jamhuriyar Nijar, Mali da Burkina Faso ke gab da kaddamar da ayyukan rundunar hadin gwiwa a karkashin inuwar kungiyar kawance ta AES, a ci gaba da jan damara a yakin da suke gwabzawa da ‘yan ta’addan yankin Sahel shekaru fiye da 10.
A baya wadanan kasashe sun kafa wata rundunar hadin gwiwa wato G5 Sahel da ta hada da kasashen Chadi da Mauritania, sai dai tsamin dangantakar da aka fuskanta a tsakanin kasashen na Sahel da Faransa ta haifar da durkushewar ayyukan rundunar.
Saurari cikakken shirin da Hassan Maina Kaina ya gabatar:
Dandalin Mu Tattauna