Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

K’asashen jamahuriyar Niger da Burkina Faso na neman sasantawa game da takkadamar kan iyaka


Judges of the International Court of Justice in The Hague, The Netherlands. (file photo)
Judges of the International Court of Justice in The Hague, The Netherlands. (file photo)

Jamahuriyar Nijer da Burkina Faso sun gabatarwa kotun duniya ta birnin Hague wata bukatar neman warware takaddamar kan iyakar da ke tsakanin su.

Kotun duniyar ta fada a jiya laraba cewa k’asashen biyu na yankin yammacin Afirka na so ne su tantance kan iyakar su da ta kama daga Tong Tong zuwa yankin Botou.

A bara ne jamahuriyar Nijer da Burkina Faso su ka amince da mik’a batun kan iyakar ga kotun duniya.

Haka kuma kotun duniyar ta ce Jamahuriyar Nijer da Burkina Faso sun yarda su tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankunan su a lokacin da su ke ci gaba da jiran hukuncin da za a yanke.

Kotun duniyar dai ita ce babbar cibiyar shari’a ta MDD kuma aikin ta shi ne sasanta rigingimun shari’ar da k’asashe ke gabatar ma ta kamar yadda ya dace da dokar k’asa da k’asa, kuma ta na bada shawarwari akan harakokin shari’ar da hukumomin MD’D da wasu k’wararrun cibiyoyi ke gabatar ma ta.

XS
SM
MD
LG