Majalisar Dinkin Duniya, tana kira ga kasashe masu bada gudumawa su kara hanu, domin a tallafawa kasashe dake fuskantar bala’in fari, a yammaci da kuma Afirka ta tsakiya,musamman ma Nijar, inda tace, kusan rabin al’umar kasar suna fuskantar mummunar yunwa.
Shugabar hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya,Josetta Sheeran,ta kira farin na Nijar da cewa annobace da take bayyana kanta yanzu,inda fiye da mutane milyan bakwai suke fuskantar karancin abinci. Haka kuma ta ce, hukumar wadata abincin zata mai da hankali kan wadanda suka fi fuskantar hadarin yunwa,‘yan yara kasa da shekara biyu. Mummunar karancin ruwan sama a bara ta janyo karancin amfanin gona ga mutum da dabba, cikin kasar.