Lahadin nan, aka fara taron kolin shugabannin Tarayyar Afirka na 15, a birnin Kampala na Uganda. An tsananta matakan tsaro.
Ministan shari’a,kuma Attorney Janar na Amurka Eric Holder zai yi jawabi ga taron, mako biyu, bayan an kai wa birnin tagwayen harin boma bomai, da suka kashe mutane 76. Ana ji Mr. Holder zai yi magana kan harin,da aka auna kan masu kallon wasan karshe na cin kofin Duniya.
Ministan harkokin wajen Uganda Okello Oryem, ya gayawa kamfanin dillancin labaran Fransa jiya Asabar cewa, matakan tsaron da aka dauka sun dara wadanda ake dauka lokacin da shugabannin kasashe suke kai ziyara.
Idan za’a iya tunawa dai kungiyar al-sahabab ce, ta dauki alhakin kai harin na ranar 11 ga watan Yuli,da cewa, harin gayya ce kan tura sojojin kasar Ugandan zuwa Somaliya, domin ayyukan kiyaye zaman lafiya.