Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Abinci Ta Duniya Tana Gaggauta Kai Agajin Abinci Zuwa Jamhuriyar Nijar


Mata su na jiran karbar agajin abincin yara a Koleram a kudancin Jamhuriyar Nijar.
Mata su na jiran karbar agajin abincin yara a Koleram a kudancin Jamhuriyar Nijar.

Hukumar ta ce tun cikin watan Mayu ta ninka yawan abincin agaji da ta ke bayarwa ga Jamhuriyar Nijar a bayan da sabuwar gwamnatin kasar ta gudanar da binciken da ya nuna cewa kashi 17 cikin 100 na yara ‘yan kasa da shekara biyar a kasar su na fama da cutar rashin wadataccen abinci mai tsanani

Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, WFP, tana gaggauta kai abinci ga yara da iyalansu su kusan dubu 700 a Jamhuriyar Nijar mai fama da fari. Rashin ruwan sama na tsawon lokaci ya nakkasa amfanin gona, ya sa dabbobi masu yawa suka mutu, ya kuma jefa mutane har miliyan 8 cikin hali na bukatar agaji.

Hukumar Abincin ta Duniya tana tura kunshin garin hatsi da masara da waken soya da kuma man girki kowane wata zuwa Jamhuriyar Nijar domin yakar rashin wadatar abincin.

Hukumar Abinci Ta Duniya Tana Gaggauta Kai Agajin Abinci Zuwa Jamhuriyar Nijar
Hukumar Abinci Ta Duniya Tana Gaggauta Kai Agajin Abinci Zuwa Jamhuriyar Nijar

Hukumar ta ce tun cikin watan Mayu ta ninka yawan abincin agaji da ta ke bayarwa ga Jamhuriyar Nijar a bayan da sabuwar gwamnatin kasar ta gudanar da binciken da ya nuna cewa kashi 17 cikin 100 na yara ‘yan kasa da shekara biyar a kasar su na fama da cutar rashin wadataccen abinci mai tsanani.

Darektan hukumar na yanki, Thomas Yanga, yace hukumar tana bukatar karin agaji domin gudanar da wannan aiki na kudi dala miliyan 213 a Nijar. Yace kashi 60 cikin 100 na wannan kudin kawai suke da shi a hannu.

XS
SM
MD
LG