Wani babban jami’in jakadancin Amurka ya ce ana bukatar Karin sojojin a Somaliya,in da ‘yan gani kashenin Islama, suke yunkurin kifar da gwamnatin riko ta kasar.
Mukaddashin sakataren harkokin wajen Amurka Johnnie Carson,ya yi taro a asirce litinin din nan da shugabannin kasashen Afirka dake gabashi,da kuma arewacin ta, a gefe daya na taron kolin Tarayyar Afirka.
Carson yace Somaliya ta zama kafar fashi a teku da ta’addanci, kuma ta zama dandali da mayakan sakai daga ketare ke zuwa domin ayarsu.
Yace shi da shugabannin kasashen Afirka da ya gana d a su, sun dukufa wajen karfafa rundunar sojoji a Somaliya da nufin murkushe al-Sahab,kungiyar mayakan sakai dake kokarin neman mai da Somaliya kasa mai bin tafarkin tsatstsaurar ra’ayin Islama.
Shugabannin Afirka suna nazarin kara karfin sojojin kiyaye zaman lafiya a Somalia, rundunar da ahalin yanzu take da dakaru dubu shida,galibi daga Uganda da Burundi. Haka kuma Tarayyar tana nazarin karawa rundunar ikon daukar matakan soji kan mayakan sakan kasar.