Kungiyar dake hankoron nazarin kare hakki da yancin Bil Adama a Syria da cibiyar ta ke kasar Britaniya, tace hare haren da Rasha ta kai jiya Talata, sune mafi muni, tun lokacinda ga gwamnatin Bashar Al Assad ta bada sanarwar a makon jiya cewa zata rage hare haren da take kaiwa da jiragen saman yaki, domin baiwa farar hula damar ficewa daga unguwani ko kuma yankunan da suke hannun ‘yan tawaye.
Tunda farko a jiya Talata, shugaban Rasha Vladimr Putin da kasashen yammaci suke ta sukar lamirin sa a saboda rawar da Rasha take takawa a Syria, ya soke ziyarar da yayi niyar kaiwa kasar Faransa. Bayan shugaban Faransa Francois Hollande ya dage cewa tattaunwar da zasu yi zai maida hankali ne akan Syria.