Duka ‘yan takarar biyu suna kokarin shawo kan rashin yarda da masu kada kuri’a suke nunawa ana kasa da wata guda a gudanar zaben shugaban kasar Amurka.
Kakakin majalissar wakilai Paul Ryan, ya fadawa wakilai ‘yan jam’iyyar Republican a wani taro da aka yi jiya Litinin cewa, ba zai kara yi wa Trump kemfe ba, ko ya kare irin magangunansa marasa dadi da yake yi wadda ke batawa masu kada kuri’a rai.
Ryan ya ce maimakon haka, zai maida hankali akan ganin an zabi ‘yan jam’iyyar Republican a majalissar wakilai domin jam'iyyar ta ci gaba da xama mai rinjaye amajalisun dokokinn Amurka. A yanzu haka dai ‘yan jam’iyyar ta Republican ne ke rike da majalissar wakilai da ta datijjai
Mutum daya daga taron na jiya ya fadi cewa Ryan bai janye goyon bayansa ga Trump ba, amma dai ba zai yi masa yakin neman zabe ba, Ryan kuma ya fadawa sauran ‘yan Republican dake majalissar cewa “ ku yi abinda kuka ga zai kaiku ga samun nasara.”.