Kamfanin ya sanar yau Talata cewa zai dakatar da sarrafa wayar baki daya ne don kiyaye lafiyar masu amfani da ita.
Tunda farko a yau kamfanin na Samsung ya bada sanar cewa ya dakatar da sayar da wayar Galaxy Note 7, ko musayar ta a fadin duniya, ya kuma yi kira ga masu amfani da ita da su daina ba tare da bata lokaci ba. Kamfanin na kasar Koriya ta kudu ya yi hasara kashi 8 cikin dari a hannayen jarinsa yau Talata.
Dama kusan wata guda ke nan ba wayar ta Note 7 a kasuwa sosai tun lokacin da kamfanin ya sanar da maido da wayoyi miliyan 2.5 saboda matsalar batiri a farkon watan Satumba. Kamfanin kuma ya ba duk masu yin amfani da wayar damar yin musaya, kafin sabbin rahotanni suka nuna cewa ko sabbin suna mugun zafin, abinda ya kawo shakka akan irin kulawar da kamfanin yake kan ingancin kere-kerensa.