Wurare da ake zaton ‘yan ta’addar ka iya kai hare haren, sun hada da inda baki ‘yan kasashen waje ke kai ziyara a yawon sun a shakatawa. Kungiyoyin ta’addanci masu alaka da kungiyar al Qaida a Afrika ta Yamma suna barazana ga yankin, a baya ma sun kai hare hare a kan jami’an tsaro da ma fararen hula a kasashen Burkina Faso da Mali.
Wata sanarwar da hukumomi suka fitarna cewa, koda yake ba a taba kaiwa kasar Ghana hari ba amma akwai bukatar a kasance cikin ko ta kwana musanman a kan iyakokin kasar da wuraren tarukan jama’a kamar wurin otal otal dake bakin teku da wuraren cin abinci da wuraren ibada.
Wannan kashedi na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Canada tace an yi ‘ya’yan kasar ta biyu.
Wani masanin sha’anin tsaro Irbard Ibrahim ya nuna rasin jin dadinsa game da yadda kasar Ingila ta fitar da irin wannan kashedi, yace da za a iya amfani da wata kafa maimako tsorata jama’a.
Mallam Irbad Ibrahim ya kara da cewa kasar Ghana bata da wata mummunar alaka da wata kasa da har zata kawo mata hari, ya kuma ce jami’an tsaron Ghana sun shirya kuma suna da kwarewar da zasu kare kasar.
Wasu ‘yan kasar sun bada mabambantan ra’ayoyi a kan wannan batu.
Wakilin mu a Ghana Ridwan Lah Muktar Abbas ya aiko mana da karin bayani:
Facebook Forum