Majalissar tsaro ta kungiyar tarayyar Afirka ta sanar da haka ne jiya Alhamis, bayan da Shugabannin masu zanga zanga, suka ki amincewa da wani tayi da Majalisar sojoji mai mulki a Sudan ta yi musu, domin samar a mafita ga makomar siyasar kasar.
Shugabannin masu zanga-zangar sunce kiran tattaunawar a da sojojin suka yi bana Tsakani da Allah bane, biyo bayan mummunan harin da aka kaiwa masu zanga-zangar a birnin Khartoum, harin da shaidun gani da ido suka zargi rundunar tsaro da aka fi sani da Rapid Support Force.
Likitocin da ke kawance da masu zanga-zangar sun ce yawan adadin mutanen da suka mutu ya haura zuwa 108 ya zuwa ranar Laraba. Ma’aikatar lafiya ta Sudan ta fadi a wata sanarwa cewa yawan wanda suka mutu bai haura 46 ba.
A Majalisar Dinkin Duniya, jakadan Afirka ta Kudu Jerry Matjila, ya fadawa manema labarai cewa Afirka ta Kudu ta bi sahun hukumomin kungiyar AU ta soke duk wata hulda da Sudan.
Ya kara da cewa Afirka ta Kudu tana kira ga dukkan bangarorin da su koma kan teburin sulhu, su kuma amince da mika mulki ga farar hula cikin gaggawa.
Facebook Forum