Kungiyar masana a kasar Sudan ta SPA atakaice, wacce ke jagorantar zanga zangar da suka iza sojojin suka kifar da gwamnatin Shugaba Omar al-Bashir, ta fada a jiya Asabar, cewa yau Lahadi ne zata bayyana matukar adawarta kuma zasu ci gaba da yin haka har sai sojojin sun mika mulki ga farara hula.
Kiran da shugabannin masu zanga zangar suke yi, na zuwa ne mako daya bayan da rundunar tsaro suka fara daukar matakan hana masu zanga zangar yin sansani a wajen helkwatan sojojin dake birnin Khartoum. Adadin mutanen da aka kashe daga ranar Litinin ya kai 113.
Kunagiyar masana a Sudan ta SPA, tace ta amince da Firai ministan Habasha a matsayin mai shiga tsakani kuma ya fara tattaunawa da gwamantin sojin kasar, koda yake kungiyar masanan ta bukaci a kafa wani bincike mai zaman kansa ya duba batun tashin hankalin da ya barke tun bayan kawar da shugaba al-Bashir
Firai ministan Habasha Abiy Ahmed, ya yi kira ga samun kwarin gwiwa yayin da ya gana da manyan sojojin masu mulkin kasar Sudan da shugabannin ‘yan adawa, a wani yunkurin kawo karshen rikicin siyasa da Sudan ta fada a cikin tun bayan hambarar da dadadden shugaban kasar Omar al-Bashir.
Facebook Forum