Firai ministan Ethiopia Abiy Ahmed, ya nuna bukatar akai zuciya nesa, yayin wata ganawa da ya yi da shugabanin sojin kasar Sudan da na ‘yan adawa, a wani yunkuri na yayyafa ruwa kan rikicin siyasar da ya mamaye Sudan, tun bayan da aka hambarar da dadadden shugaban kasar Omar Al Bashir.
"Dangane da sakamakon tattaunawar da aka kwashe yini guda ana yi, za a iya cewa an samu ci gaba.” In ji mai magana da yawun Ahmed, Billene Seyoum.
Shi dai shugaban na kasar ta Habasha, ya jima yana shan yabo kan yadda ya sasanta rikicin da ke tsakanin kasarsa da makwabiyarta ta Eritrea, wacce suka dade sa ba ga maciji.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne, Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU ta dakatar da Sudan daga kungiyar, ta kuma yi barazanar saka mata tsauraran takunkumi, muddin sojojin kasar ba su yi maza sun mika mulki ga farar hula ba.
Facebook Forum