A Sudan an rufe shaguna yayin da tituna suka kasance wayam a Khartoum babban birnin kasar, a rana ta farko da shugabannin masu zanga zanga suka yi yekuwar a fara yajin aikin gama-gari, a wani mataki na neman majalisar sojin da ke jagorantar gwamnatin wucin gadin kasar ta Sudan ta yi murabus.
Kamfanin dillancin labarai na AP, ya ruwaito cewa kungiyar kwararrun ma’aikata da aka fi sani da SPA, ta yi kira ga jama’a da su zauna a gida a yau Lahadi, a wani kokari na nuna fushi kan yadda dakarun kasar suka far wa masu zaman dirshan a wajen hedkwatar dakarun kasar da ke Khartoum a makon da ya gabata.
“Dukkanmu muna fatan za a mika mulki ga farar hula, amma wasu sun sha alwashin hakan ba za ta yi wu ba, jami’an tsaron RSF sun hana mutane bayyana ra’ayinsu.” In ji Khodar Salah, wani mazaunin birnin na Khartoum ne.
Kungiyar ta SPA dai, ita ta jagoranci zanga zangar da aka kwashe watanni ana yi, wacce ta yi sanadin hambarar da gwamnatin shugaba Omar Sal Bashir a watan Afrilun da ya gabata, inda ta kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da kasancewa a tituna har sai an mika mulki ga farar hula.
Facebook Forum