‘Yan sandan kasar Australia na tuhumar wani babban jigon fadar Paparoma dake Vatican da laifin yin lalata.
Hukumomi dai ba su ba da wani karin bayani akan zarge-zargen da ake yi wa Cardinal George Pell ba, baya ga cewa an sami korafe-korafe da yawa kan masu alaka da zargin.
A yanzu dai an umurci Cardinal Pell, wanda ya taba zama babban mai ba Paparoma Francis shawara akan harkokin kudi, ya bayyana gaban wata kotu a birnin Melbourne ranar 18 ga watan Yuli.
A wani taron manema labarai da aka yi a fadar Vatican, Pell ya fadi cewa bai aikata laifukan da ake tuhumarsa da su ba, kuma an dade ana kokarin a zubar mai da mutunci.
Cardinal Pell dai shi ne kusar Katolika a fadar Paparoma mafi babban mukami da aka taba zargi da irin wannan laifi mai alaka da jima’i a tarihin fadar.
Facebook Forum