Wani bayanin da rundunar sojin Turkiyya ta fitar na ikirarin cewa gwabzawar da aka yi tsakanin rundunar sojin kasar Turkiyya kurdawan ta faru ne a wajejen Afrin.
Kungiyar mayakan Turkiyya ta YPG wata muhimmiya ce a hadakar dakarun Siriya masu ra'ayin dimokaradiyya wadanda Amurka ke goya ma baya musamman ma game da yakin neman fatattakar ISIS daga tungarsu da ke Raqqa.
To amma Turkiyya na matukar adawa da mayakan Kurdawa, wadanda ta ke ma ganin gyauron haramtacciyar Kungiyar Ma'aikata ta Kurdawa, PKK a takaice, wadda ta shiga yakin sunkuru a kudu maso gabashin kasar tun daga 1980.
Cikin gudunmuwar da Amurka,ta baiwa kungiyar YPG har da wasu makamai, wadanda Turkiyyar ke tsaron yiwuwar su fada hannun mayakan PKK.
Gwamnatin Turkiyya, ta ce Sakataren Tsaron Amurka Jim Mattis, ya ba ta tabbacin cewa Amurka za ta karbo makaman da zarar an kwato Raqqa, to amma Mattis ya bayyana cewa goyon bayan da Amurka ke baiwa kungiyar YPG zai dore.
Facebook Forum