Shirin zai yi garambawul ga tsarin tallafin abinci, da muhalli, da sauran tsare tsaren agazawa marasa karfi.
Sabon shirin nasa zai bukaci wadanda suke samun irin wannan tallafi su yi wasu ayyuka, sannan kuma shirin zai sakarwa jihohi mara wajen amfani da tallafin da gwamnatin tarayya take bayarwa domin tallafawa talakawa.
Da yake jawabi jiya Talata a nan birnin Washington, Ryan yace, "Abunda shirin nan zai samar shine sabuwar hanyar yaki da talauci, wanda zai sake farfado da manufar tsamo mutane daga kangi, da kuma maganin sarsalar talauci."
Amma wasu 'yan jam'iyyar Democrat, da wasu masana, da wasu kwararru sun yi watsi da shirin da kakakin majalisar Ryan ya gabatar.
"Abin bakinci, karkashin wadannan kalamai masu dadi da aka bayyana yau, 'yan Republican suna gabatar da shirin da aka sansu da shi maras imani, na a yi jiran tsammani da suka yi shekaru suna gabatarwa," inji shugabar marasa rinjaye a majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi, daga jihar California.