Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican, Donald Trump, da kakakin majalisar wakilai Paul Ryan, sun amince zasu gana makon gobe, amma babu alamun dan takarar mai jiran gado, yana da kwarin guiwa kan ganawar.
Trump yace bai sani ba, ko tattaunawar da za'a yi da nufin hada kan 'yan jam'iyyar, bayan da ya sami nasara, zata haifar da da' mai ido ba, kuma hakan bai dame shi ba. "abunda yafi zama muhimmi shine miliyoyin mutane da suka fito suka zabe ni, suka bani gagarumar nasara a kusan dukkan jihohi."
Trump yace yace, ya gayawa shugaban jam'iyar Reince Priebus cewa, kalaman Paul Ryan, na kin yi masa mubaya, "bai dace ba sam-sam," duk da haka, ya amince da bukatar da shugaban n jam'iyyar ya gabatar na yin wannan ganawar.
Ryan, ya fada jiya jumma'a cewa, shi da wasu shugabannin jam'iyyar Republican a majalisar wakilai, zasu gana da Trump, ranar Alhamis, da safe.
Yace tattaunawar zata maida hankali kan "irin manufofin jam'iyyar da zasu sami karbuwa ga Amurkawa a zaben kasa da za'a cikin watan Nuwamba."
Rahotanni sun nuna cewa, ba Ryan ne kadai yaki goyon bayan dan kasuwan, wanda yanzu yake zaman dan takarar shugabancin kasa karkashin inuwar jam'iyyar ba.
Kamar yadda jaridar Wall Street Journal ta fada, wakilai 12 ne cikin 'yan majalisar wakilai data dattijai 300, 'yan Republican ne suka bayyana goyon baya ga Donald Trump, a tsakanin gwamnoni 31 a karkashin jam'iyyar kuma, mutum 3 ne kadai suka bayyana goyon bayansu ga Mr.Trump.
Shugabannin Amurka biyu na baya bayan nan karkashin jam'iyyar, George Bush babba da karami, sunce ba zasu sa baki a yakin neman zaben jam'iyyar na bana ba.
Haka nan 'yan takarar neman shugabancin jam'iyyar biyu na baya bayan nan, John McCain a 2008, da kuma Mitt Romney a 2012, suma sunce ba zasu halarci babban taro na jam'iyyar da za'a yi cikin watan Yuli ba.
Da yake magana, shugaban Amurka Barack Obama, yace tilas masu zabe "su maida hankali sosai" kan kalaman da dan takarar shugabancin na Amurka mai jiran gado Donald Trump, da wasu sauran 'yan takara suke yi, a magana da yayi jiya jumma'a.
"Wannan ba nishandantatta mutane bane. wannan ba wasan kwaikwayo bane.Obama ya fadawa manem alabarai.