Tace mutumin hadari ne. Ta fadi haka ne a wani jawabi da ta yi kan harkokin waje mai tsanani da ta gabatar jiya Alhamis, a birnin San Diego, na jihar California.
"Bashi da kan-gado, bai dace da rike mukamin da yake bukatar ilimi, da natsuwa ba. Aiki yana tattare da matukar nauyi, inji Madam Hillary."Wannan ba mutum bane da har a bari ya rike ikon amfani da makaman nukiliya."
Hillary Clinton ta ci gaba da cewa, Trump "bai san Amurka ko ma duniya ba." Ba abun mamaki bane idan Trump ya jefa mu cikin yaki domin kawai wani ya caccake shi, ganin mutum ne da bashi da juriya.
Trump wanda kamar dama yana dakon jawabin nata ne, ya soki abokiyar takararsa ta jam'iyyar Democrat a dandalin Twitter cewa, Hillary a zaman wacce bata da gaskiya, ya ci gaba da cewa, wacce zan kira "Hillary makaryaciya, tana shirin zata shirga matsayina kan harkokin waje," ya rubuta.
Clinton ta nuna kwarewarta tun tana uwargidan shugaban kasa,senata, da kuma sakatariyar harkokin wajen Amurka, tace shugabancinta zai samar da difilomasiyyar da Amurka take bukata domin dorewa.
Ahalinda ake ciki, kuma, kakakin majalisar wakilan Amurka Paul Ryan, daga karshe ya bayyana goyon bayansa ga takarar Mr. Trump.