An gudanar da bikin jana’izar tsohon gwamnan jihar Taraba Danbaba Suntai a karamar hukumar Bali ta jihar Taraba.
Shugabannin gargajiya a Najeriya na ci gaba da kiraye-kirayen zaman lafiya da hadin kan kasa yayin da ake kai ruwa rana tsakanin masu neman kafa kasar Biafra da kungiyar matasan arewa da ke cewa al’umar Igbo su tattara inasu-inasu su koma yankunansu tunda suna son bangarewa.
Gwamnatin jihar Taraba ta tanadi kayayyakin abinci a wani mataki na ragewa talakawanta radadin hauhawar farashi kayan, don rabawa ga dukkan mazabunta dake kananan hukumomi goma sha shida albarkacin watan azumi.
Kimanin wata daya da kafofin yada labarai a Najeriya suka ba da labarin kakaki majalisar jihar Adamawa Kabiru Mijinyawa, ya yi wa sajen Umaru Dan sanda mai tsaron lafiyarsa duka, lamarin da rundunar yan sandan ta ce tana gudanar da bincike a kai.
Gidauniyar tallafawa jihohin arewa maso gabas da gwamnatin jihar Adamawa, sun saka hanu kan yarjejeniyar aiki kafada da kafada ta naira miliyan arba'in don sake gina asibitocin Michika da Mubi.
Kungiyar malamai ta kasa reshen jihar Adamawa ta ce dokar ta baci da gwamnatin jiha ta ayyana watanni shida da suka gabata bata yi tasiri ba.
Kungiya ma’aikata masu sarrafa wutar lantarki ta ‘kasa reshen arewa maso gabas ta ce mambobinta shida sun rasa rayukan su, saboda rashin kariya a lokacin da suke bakin aiki sakamakon sakaci da neman riba fiye da kima.
‘Yan gudun hijira sama da 3000 sun koma muhallansu a karamar hukumar Madagali dake jihar Adamawa, sakamakon nasarar da rundunar soja ke samu na dakile hare-haren kunar bakin wake da na sari ka noke.
Shirin daukar malamai 3000 aiki na tsawon wa’adin shekaru biyu ana biyansu albashin Naira 30,000 ga masu digiri, da kuma Naira 20,000 ga masu NCE da gwamnatin jihar Taraba ta kuduri aniyar yi ya gamu da shakku, ganin cewa tana fuskantar matsalar biyan albashi a jihar.
Yan fashi da makami sun kashe wasu ma’aikatan tawagar Majalisar Dinkin Duniyar biyar a garin Koncha na Jumhuriyar Kamaru, dake kan iyakarta da Najeriya, hakan ya faru ne a lokacin da suka je yankin aikin shata kan iyakokin kasashen biyu.
An sake bude sansanin horas da masu yiwa kasa hidima na Yola fadar jihar Adamawa, bayan rufe shi shekaru uku da suka gabata sakamakon rikicin Boko Haram.
Kungiyar kwadago ta jihar Adamawa ta ce malaman firamare da jami’an kiwon lafiya matakin farko ba su anfana daga tallafin Naira Biliyan 9.5 da gwamnatin tarayya ta samar shekarar da ta gabata don rage bashin albashin da ma’aikata ke bin gwamnati jiha.
Mata ‘yan gudun hijira Musulmai da Kirista dubu biyu da dari biyar sun anfana da tallafin abinci albarkacin bukin Kirismeti a Yola fadar jahar Adamawa.
Sakamakon nasarorin da kungiyar wanzar da zaman lafiya tsakanin mabiya addnin Krista da Musulmai ta kasa da kasa ta cimma bayan rarrabuwar kawuna da rikicin Boko Haram ya haddasa a Arewa maso Gabashin Najeriya, kungiyar hadin kan kasashen nahiyar Afirka ta baiwa wannan kungiya kujera a kwamitin sulhun ta.
Matasa 3,811 ne suka anfana daga shirin gwamnatin tarayya mai lakabi da N-Power Progromme rukunin farko a jihar Adamawa.
Kimanin mutane 30 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar tashin bam a kasuwa Magali dake jahar Adamawa.
Yau ce Ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yin dubi kan irin halin da nakasassu ke ciki a duk fadin duniya.
Kungiyar direbobin Tirelolin masu dakon shanu daga kasuwar shanu ta kasa da kasa na garin Mubi, dake jihar Adamawa sun yi barazanar shiga yajin aiki saboda abin da suka kira tsangwama da cin mutunci da gallazawa na jami’ian tsaro akan hanyoyi don karbar na goro.
Domin Kari