Kowace shekara, mujallar ta U.S. News & World Report, ta kan gwada manyan jami'o'i fiye da 1,800 na Amurka, ta wajen amfani da mizanai da dama don gane wacce ce tafi sauran.
A wannan shekarar dai jami'ar dake sahun gaba ita ce Jami'ar Princeton. Ta biyu ita ce Jami'ar Harvard. Jami'o'in Chicago da Yale ne su ka yi na uku tare.
Idan kuma saboda wasu dalilai, wadannan kwalejojin ba su kayatar ba, to wannan binciken ya kuma wallafa Kwalejojin da ba na kimiyya ba, da jami'o'in yankuna da Kwalejojin yankuna da kuma Kwalejoji da Jami'o'in da bisa tarihi na Bakake ne.
Wani abin da ya banbanta binciken wannan karon da wadanda su ka gabata shi ne, a bana kuma a karon farko, an yi la'akari da girman aji da yawan dalibban dake cikinsa.