Duk da cewar an fara samun kwanciyar hankali, akwai fadace fadace nan da can, Sakatare Kerry ya fada a jiya Litinin cewa , ba za a yi saurin tabbatar da ingancin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka kulla tsakanin Amurka da Rash aba tukuna.
A ranar Asabar ne Sakatare Kerry da mininstan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov suka bayyana yarjejeniyar a Geneva, kuma yarjejeniyar ta samu goyon bayan wasu kasahe kamar Iran wacce take goyon bayan gwamnatin Syria da kuma Turkiya wacce ita kuma take son ganin an tsige shugaba Bashar al Assad daga mulki.
Idan aka yi mako daya da tsagaita wutar karkashin wannan yarjejeniya, hakan zai yi sanadiyar Amurka da Rasha su hada kai wurin kai farmaki ta sama a kan mayakan IS da al-Nusrat wacce ke kiran kanta da Jabhat Fateh al-Sham da aka dauketa reshen kungiyar al-Qaida.