Kungiyar Kasashen Larabawa dake yankin Gulf, ta nuna damuwarsu kan wani kudiri da Majalisar Dokokin Amurka ta amince da shi, wanda zai baiwa iyalan wadanda suka mutu a harin ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2001, su shigar da gwamnatin Saudiyya kara, bisa zargin sun marawa aikin ta’addancin baya.
Kungiyar mai mabobi shida a Majalisarta, wacce Saudiyya babbar mamba ce, ta ce kudirin da Majalisar dokokin Amurkan ta amince da shi, ya sabawa ka’idojin kawance da ke tsakanin kasashen.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne, majalisar wakilan Amurka ta amince da wannan kuduri, duk da barazanar da Fadar White House ta yi na cewa za ta yi amfani da karfin da doka ta bata domin yin watsi da kudurin.
Ita dai Majalisar Dattawan Amurka tun a watan Mayu ta amince da wannan kuduri, wanda zai ba da damar hukunta mai daukar nauyin ayyukan ta’addanci.